Duniya

Fada ya barke tsakanin Armenia da Azerbaidjan

yankin  Nagorny Karabakh da kasashen biyu ke fada a kai
yankin Nagorny Karabakh da kasashen biyu ke fada a kai KAREN MINASYAN / AFP

Hukumomin Azerbaidjan sun sanar da kama wasu kauyukan Armenia bayan da suka gwabza fada da dakarun Karabakh yan aware dake samun goyan bayan kasar Armenia.Hukumomin kasar Armenia a daya geffen sun musanta labarin kama wasu yankunan daga Azerbaidjan.An dai bayyana mutuwar mutane 23 yanzu haka.

Talla

Mabanbantan sanarwar kasashen biyu da ke kudancin Caucasus a yau lahadi, Azerbaijan ta ce dakarun Sojinta sun kwace wasu yankuna, yayinda Armenia ta sanar da karbe wasu yankuna daban.

Tun bayan kwace ikon da Armenia ta yi da yankin ‘yan awaren Azarbaijan na Nagorny Karabakh da ke kudu maso yammacin kasar ne ake ci gaba da fuskantar takun saka wanda har ya kai ga yakin shekaru tsakanin 1990, amma kuma sai a wannan karon ne rikici ke kara tasowa gadan-gadan duk da cewa dai ko a shekarun baya kasashen na harin sari ka noke tsakaninsu.

Kasashen Duniya na ci gaba da kira ga kasashen Armenia da Azerbaijan na ganin sun tsagaita wuta tareda shifuda hanyoyin shiga sulhu domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Faransa ta bakin Ministan harakokin wajen kasar ta yi kira ga kasashen biyu, Rasha da Amurka sun bayyana shirin su na shiga tsakani don ganin an kawo karshen wannan matsalla cikin ruwan sanyi.

Yanzu haka ,rahotanni na nuni cewa Rasha ce kasar dake sayar da makamai ga kasashen biyu tsawon shekaru 30, ana mata kallon wacce za ta iya shiga tsakani don warware wannan rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.