Sama da mutane miliyan 60 suka kamu da korona a India-Rahoto

Ma'aikatan kiwon lafiya dake kula da annobar korona a kasar India
Ma'aikatan kiwon lafiya dake kula da annobar korona a kasar India Dibyangshu SARKAR / AFP

Wani bincike ya nuna cewar  kimanin mutane sama da miliyan 60 suka kamu da cutar korona a kasar India, sabanin miliyan 6 da hukumomi suke bayarwa a hukumance.

Talla

Alkaluman gwamnatin Indiya na nuna Kasar mai yawan al'umma biliyan 1 da miliyan 300, ita ce kasa ta biyu a duniya dake da adadi mafi yawa na wadanda suka harbu da cutar coronavirus, da sama da mutane miliyan 6 da dubu 100, bayan Amurka.

To saidai binciken da wasu sassan hukumomin lafiyar kasar suka gudanar a baya bayan nan na nuna ainahin adadin ka iya zarce haka fiye da yadda ake zato.

A taron manema labarai da aka gudanar a Kasar, Babban Darekta janar na hukumar binciken magunguna na India ICMR, Balram Bhargava ya sanar da cewa bincikensu na nuna a cikin kowanne yaro daya cikin yara 15 masu shekaru 10 da sama ya harbu da annobar a daga watan Agusta da ya gabata.

Bhargava ya ce binciken ya bayyana cutar ta fi yaduwa a yankunan talakawa dake tsakiyar birane da kashi 15.6 sabanin yankunan masu galihu dake tsakiyar birane da kashi 8.2, saidai a karkara binciken ya nuna kashi 4.4 na mutane kadai ne suka harbu da cutar.

An dai karbi samfurin jinin mutane sama da dubu 29 daga jahohi 21 tsakanin tsakiyar watan Agusta zuwa tsakiyar watan Satumban nan dake karewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.