Rabin al'ummar Karabakh sun tserewa gidajensu saboda kazamin farmaki

Sojojin Azerbaidjan a yankin Karabakh
Sojojin Azerbaidjan a yankin Karabakh Ministère de la Défense azerbaïdjanais

Rabin al’umar yankin Nagorny Karabakh sun kauracewa gidajensu sakamakon yakin da ake gwabzawa tsakanin 'yan awaren yankin armeniyawa, da dakarun kasar Azerbaïdjan, kamar yadda mahukumtan yankin suka sanar a yakin da shugaban Rasha Vladimir Poutine ya danganta da alkaba’i.

Talla

Kungiyar agaji ta duniya Croix-Rouge da ke wakiliyar kasashen Faransa, Amruka da Rasha a shiga tsakanin sasanta rikicin, ta ce tun bayan barkewar yakin a ranar 27 ga watan Sutunba da ya gabata, fararen hula da dama ne yakin ya rutsa, da yanzu haka ke cikin mawuyacin hali a yankin na Nagorny Karabakh.

Bangarorin biyu dake rikicin sun yi kunnen kashi kan kiraye kirayen da ake yi masu na tsagaita wuta da suke budawa juna.

Shugaban Rasha Vladimir Poutine ya danganta yakin da zama wani babban alkaba’i, inda ya yi kira tare da jaddadawa cewa a tsagaita wuta. Kuma a cikin gaggawa.

A kwana na 11 da barkewar yakin  a kalla kashi 50% na al’ummar yankin Nagorny Karabakh sun fice daga cikinsa, kuma kashi 90% daga cikinsu mata ne da kananan yara, kamar yadda mai shiga tsakanin yankin da ya ayyana kansa jamhuriya mai cin gashin kai Artak Belgarian ya sanar da AFP , inda ya ce mutanen da suka tsere kawo yanzu sun tasarma dubu 70.000 zuwa 75.000.

Yankin Nagorny Karabakh dai na kunshe ne da kimanin mutane dubu 140.000, kuma kashi 99% yan kabilar Arméniyawa ne zalla, a yayin da tuni yan kabilar Azéris suka tsre daga yankin tun lokacin yakin da aka gwabza na shekarar 1990.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.