Korea ta Arewa

Kim Jong Un ya jagoranci gwajin sabbin makamai yayin atisayen Sojin kasar

Shugaba Kim Jong-un na Korea ta Arewa.
Shugaba Kim Jong-un na Korea ta Arewa. REUTERS

Shugaba Kim Jong Un na Korea ta Arewa ya jagoranci wani aggarumin atisayen Soji yau Asabar da ke da nufin nuna yadda kasar ke zaune lafiya ba tare da ko da mutum guda da ya kamu da annobar cutar coronavirus ba, duk da yadda cutar ke ci gaba da kisa a sassan Duniya.

Talla

Atisayen wanda ya kai ga gwajin wasu sabbin makamai masu linzami da ke cin dogon zango wanda masana suka bayyana a mai matukar hadari, dubunnan sojojin kasar ne suka gudanar da faretin Sojin ba tare da koda mutum guda sanye da mayanin rufe hanci da baki ba.

A jawabinsa lokacin da ya ke sanya ido wajen gwajin makaman Kim Jong Un ya ce wajibi ne su kara karfinsu na Soji don tabbatar da tsaron kasarsu.

Tun a farkon shekarar 2019 ne sabuwar alakar da ake fatar kullawa tsakanin Amurkan da Korea ta Arewa ta zo da baraka, batun da ya bai wa Kim damar ci gaba da aikin gwaje-gwajensa na makaman nukiliya ko da ya ke a wannan karon yana gwajin ta sigar Diflomasiyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.