Iran

Wa'adin takunkumin hana mu cinikin makamai ya kare - Iran

Wasu daga cikin makamai masu linzami da Iran ta kera a birnin Teheran.
Wasu daga cikin makamai masu linzami da Iran ta kera a birnin Teheran. ATTA KENARE / AFP/File

Iran ta ce wa’adin takunkumin da majalisar dinkin duniya ta kakaba mata na haramcin saye ko sayar da makamai ya kare a yau lahadi, kamar yadda yake a rubuce cikin yarjejeniyar da ta cimmada manyan kasashen duniya a shekarar 2015 kan shirinta na nukiliya.

Talla

Iran ta kuma ce a karkashin yarjejeniyar nukiliyar ta 2015, karewar wa’adin takunkumin hana cinikin makaman zai zai soma aiki ne ba tare da bukatar cika wasu sharudda ba.

Cikin sanarwar da ta fitar, ma’aikatar harkokin wajen Iran, ta ce daga yau, Iran na da ‘yancin sayen dukkanin makaman da basu saba dokokin kasa da kasa ba don tsaron kanta, ba tare da fuskantar wani cikas ba.

A watan Agustan da ya gabata na wannan shekara, Amurka ta yi yunkurin ganin majalisar dinkin duniya ta tsawaita wa’adin haramtawa kasar ta Iran cinikin makamai, amma ta gaza samun goyon bayan manbobin kwamitin tsaron majalisar.

Sai dai tuni Amurkan ta yi gaban kanta wajen sake kakabawa Iran din sabbin takunkuman karya tattalin arziki a lokuta daban daban kan shirin nukiliyarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.