Iran

Iran ta sha alwashin sayar da makamai fiye da yadda take saye

Shugaban Iran Hassan Rohani,
Shugaban Iran Hassan Rohani, REUTERS/Brendan McDermid

Kasar iranta bayyana cewa, zata fi sayar da makami fiye da saya, bayan da ta bayyana kawo karshen wa’adin dogon takunkumin da Majalisar dinkin duniya ta kakaba mata kan hana sayar mata da manyan makamai a duniya

Talla

Mahukuntan Tehran sun bayyana cewa haramcin da aka yi masu na saye da sayar da makamai a duniya ya kawo karshe ne nan take a ranar Lahadi, 18 ga watan Oktoba sakamakon yarjejeniyar da ta cimma da kasashen duniya a 2015 kan shirinta na nukliya kafin kasar Amruka ta janye daga cikin yarjejeniyar

Kafin ta sayi makaman a matakin farko, Iran na da karfin samar da makaman ne ga kasashen duniya kamar yadda kakakin ma’aikatar harakokin wajen Iran, Saeed Khatibzadeh.

Cire takunkumin dai zai bai wa Iran damar saye da sayar da makamanta da kuma kayayakin aikin soja, musaman ma tankokin yaki da motoci masu sulke, jiragen saman yaki Helikoptoci da kuma makaman atilare masu nauyi.

A cewar Khatibzadeh, iran za ta shiga cikin kasuwar saye da sayar da makamai ta hanyar dattako da sanin ya kamata ga sauran kasashen duniya bisa tsarin lisafinta na kashin kai.

Takunkumin hana saye da sayarwa iran makamai dai ya kamata ya kawo karshen aikinsa ne daga ranar jiya lahadi 18 ga watan octoba, kamar yadda kudirin MDD kan yarjejeniyar Nukliyar da kasar ta Cimma da manyan kasashen duniya a 2015 ya tanada

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.