Sojojin Armenia sun kashe mata da fareren hula a yankin Karabakh

Dakarun sojin Armenia
Dakarun sojin Armenia Vahram Baghdasaryan/Photolure via REUTERS

Gwamnatin Azerbaijan tace dakarun Armenia sun halaka mata fararen hula sama da 20 da jikkata wasu da dama, bayan harin makamai masu linzamin da suka kai kan yankinta na Barda dake gaf da Nagorno Karabakh.

Talla

Farmakin baya bayan nan dai shi ne mafi muni daga cikin makamantasa da rahotanni suka tabbatar, tun bayan barkewar sabon yaki a watan jiya, tsakanin kasashen na Armenia da Azerbaijan kan mallakar yankin na Nagorno Karabakh.

Fadar gwamnatin Azerbaijan tace harin dakarun Armenia na makamai masu linzami kan yankin Barda ya kasha fararen hula 21, tare da jikkkata wasu akalla 70.

Sai dai cikin sanawar da ta wallafa a shafinta na Facebook, ma’aikatar tsaron Armenia ta musanta kai farmakin.

Kawo yanzu dai sama da mutane dubu 1 ne suka rasa tun bayan barkewar sabon yakin tsakanin Armenian da Azerbaijan a ranar 27 ga watan Satumba, kuma alkaluma sun nuna cewar mafi akasarin mamatan mayakan Armenia ne, sai kuma fararen hula daga dukkanin kasashen 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.