Harin ta'addanci a jami'ar Afghanistan ya hallaka mutane 19

Mutane akalla 19 suka rasa rayukansu yayin da wasu 22 suka jikkata sakamakon wani harin ta’addanci da aka kai jami’ar birnin Kaboul na kasar Afghanistan.

'Yan sandan Afghanistan a wajen da aka kai hari jami'an Kaboul
'Yan sandan Afghanistan a wajen da aka kai hari jami'an Kaboul AP Photo/Rahmat Gul
Talla

Majiyar hukumomin da na Shaidun gani da ido duk sun tabbatar da cewa, mutanen dake dauke da makamai sun kutsa kai ne a cikin jami’ar ta birnin Kabul, inda suka shiga bude wuta kan mai uwa da wabi al’a’marin da ya haifar da guje gujen dalibai.

kakakin ma’aikatar cikin gidan Tariq Arian ya danganta maharan da zama makiya ci gaban kasar ta Afghanista da harakokin Iliminta.

A nasa bangaren kakakin 'yan sandan Kabul Ferdaws Faramerz, ya sanar da AFP cewa mafiya yawan wadanda suka rasa rayukansu dalibai ne.

kakakin ofishin ministan ilimin kasar ta Afghanistan Hamid Obaidi, ya sanar da cewa, an kaddamar da harin ne a dai dai lokacin da wani babban jami’in gwamnatin kasar ta Afghanistan ya ziyarci jami’ar domin kaddamar da bikin baje kolin litattafan Ilimi mai zurfi na Kasar Iran.

Tuni dai kungiyar Taliban dake ci gaba da tattaunawar neman zaman lafiya da gwamnatin Afghanistan karkashin jagorancin kasar Amruka ta nisanta kanta da harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI