Franministan Bahrain da yafi dadewa a duniya ya mutu yana da shekaru 84

Faraministan da yafi dadewa a duniya, Khalifa bin Salman na kasar Bahrian ya mutu yana maishekaru 84 a Duniya bayan ya kwashe shekaru 50 Yana mulkin kasar.

Franministan Bahrain Khalifa Bin Salman al-Khalifa
Franministan Bahrain Khalifa Bin Salman al-Khalifa REUTERS/Athit Perawongmetha
Talla

Khalifa bin Salman wanda shine yafi dadewa akan kujera Faramista a Duniya ya dare karagar mulki tun a shekarar 1971, lokacin da kasar ta samu inci kai, kuma an haifeshi ne a shakarar 1935, ya rasu yana da shekaru 84, Kamar yadda wata kafar yada labaran kasar ta sanar.

Khalifa Bin Salman mutun ne mai wuyar sha’ani a tsawon mulkinsa na shekaru 50, a kasar da jagoririnta mabiya akidar sunni ne, amma mafiyawan al’umar kasar mabiya  shi’ane.

A shekar 2011, mabiya shi’a a kasar sun gudanar da zanga zanga tsawon wata daya suna neman yayi murabus, Kamin sojojin kasr Saudiya dake mara masa baya su fatatakesu.

A tsawon mulkinsa ya taka muhimmiyar rawa a fagen siyasa kasar, da tatalin arziki, da kuma hulda da kasashen ketare.

Shugabanin yankin Gulf na jinjinamasa kan tsawon mulkinsa wanda tarihi bazai manta dashi ba.

Ya mutune a wata asibiti dake kasar Amurika, kuma za ayi janaizarsa da zaran ankawo gawarsa gida, kuma yanzu haka anshiga zaman makoki na kwanaki ukku a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI