Afrika

Shugaba Ouattara ya gana da jagoran yan Adawa

Shugaban Kasar Cote d’Ivoire Alassane Ouattara ya gana da babban dan adawan kasar Henri Konan Bedie inda suka yi alkawarin tabbatar da zaman lafiya, bayan tashin hankalin da ya biyo bayan zaben kasar wanda ya kai ga rasa rayuka.

Alassane Ouattara  da  Henri Konan Bédié a Otel du Golfe na Abidjan
Alassane Ouattara da Henri Konan Bédié a Otel du Golfe na Abidjan REUTERS/Luc Gnago
Talla

Bayan ganawar shugabannin biyu a Otel du Golfe dake Abidjan ,yan siyasar sun shaidawa manema labarai cewar, wannan mataki ne na farko dangane da aniyar su ta tabbatar da zaman lafiya a kasar, inda suka yi alkawarin cigaba da tintibar juna.

Ministan sadarwar kasar Sidi Tiemoko Toure ya sanar da cewar mutane 85 aka kashe a tashin hankalin da aka samu, yayin da 484 suka samu raunuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI