Armenia-Azerbaijan

Mun rasa dakaru sama da dubu 2 a rikicin Nagorno-Karabakh - Armenia

Gwamnatin Armenia ta ce mayakanta akalla dubu 2 da 317 ne suka rasa rayukansu, yayin yakin da suka gwabza da sojojin Azerbaijan kan rikicin mallakar yankin Nagorno-Karabakh.

Wasu sojojin Rasha, yayin aikin wanzar zaman lafiya na shiga tsakanin rikicin Armenia da Azerbaijan kan yankin Nagorno-Karabakh
Wasu sojojin Rasha, yayin aikin wanzar zaman lafiya na shiga tsakanin rikicin Armenia da Azerbaijan kan yankin Nagorno-Karabakh AFP
Talla

Rahoton ma’aikatar lafiyar kasar ta Armenia ya nuna karuwar dakarun da ta rasa a yakin kusan watanni biyu tsakanin ta da Azerbaijan da adadin dubu guda.

Sai dai har yanzu Azerbaijan ba ta bayyana nata adadin dakarun da ta rasa a yakin ba.

A karshen makon nan Rasha ta yi nasarar jagorantar cimma yarjejeniyar kawo karshen rikicin, wadda a karkashinta Armenia ta amince da mikawa Azerbaijan yankuna da dama a yankin na Nagorno-Karabakh.

A jiya Juma’a shugaban Rasha Vladmir Putin ya ce jumillar mutanen da suka rasa rayukansu a yankin na Armenia da Azerbaijan ya zarta dubu 4000, ciki har da fararen hula kusan 150, yayin da kuma wasu sama da dubu 8 suka jikkata, baya ga wasu dubban da suka rasa muhallansu.

Rahotannin baya bayan nan daga yankin na Nagorno-Karabakh sun ce mazauna kauyukan dake yankin da dama sun cinnawa gidajensu wuta a yau asabar, kafin ficewa daga kauyukan, yayinda Armenia ke shirin cika alkawarin mikawa Azerbaijan ikon mallakar yankunan kamar yadda suka cimma a yarjejeniyar sulhun da Rasha ta jagoranta a makon nan da ya kare.

A karshen makon nan mazauna kauyen Kalbajar dake yankin na Nagorno-Karabkh suka soma barin muhallansu, bayan shafe gwamman shekaru suna karkashin ikon ‘yan aware magoya bayan Armenia, sai dai a gobe Lahadi gwamnatin Armenia za ta mikawa Azerbaijan yankin, bayan kawo karshen yakin da suka gwabza tsawon kusan watanni biyu, kan mallakarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI