Yeman zata fuskanci yunwar da ba'a taba ganin irinsa ba - Guterres

Sakatare Jnar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Sakatare Jnar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres REUTERS/Lisi Niesner

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce, kasar Yemen da yanzu haka yaki ya daidaita na cikin hadarin fuskantar tsananin yunwa irin wanda duniya bata taba gani ba cikin shekaru da dama.

Talla

Babban magatakardar yace, idan har ba’a dauki matakin gaggawa na taimawa kasar ba to miliyoyin rayuka na iya salwanta a kasar da ta jimre yakin shekaru biyar da ake fafatawa tsakanin 'yan tawayen Huthi da ke samun goyon bayan Iran da sojojin gwamnati.

Gwamnati a Yemen na samun goyon bayan kawancen da Saudiyya ke jagoranta, wadanda ke samun taimakon kasashen Yammacin Turai ciki har da Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.