Myanmar na ci gaba da musgunawa musulmin Rohingya- Lauyoyi
Wallafawa ranar:
Lauyoyin da ke kare mutanen da aka ci zarafin su a kasar Myanmar sun ce har yanzu gwamnatin kasar na cigaba da aikata laifuffukan yaki akan 'yan kabilar Rohingya Musulimi sabanin umurnin kotun duniya.
Kotun duniya ta ki amincewa da matsayin jagorar gwamnatin Myanmar Aung san Suu Kyi, inda ta bada umurnin dakatar da daukar duk wani mataki da zai musgunawa Rohingya da kuma lalata shaidun da ake da su dangane da karar da aka shigar akan su.
Tun Khin, shugaban kungiyar Yan kabilar Rohingya mazauna Birtaniya yace har yanzu babu abinda ya sauya dangane da cin zarafin da gwamnati ke yi.
Irin wannan kazamin harin ya hallaka daruruwan Rohingya da kuma tilastawa kusan 750,000 barin matsugunin su a shekarar 2017.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu