Nagarno-Karabakh

Armeniyawa na neman adawo da sojojin da suka bace a yankin Nagarno-Karabakh

Masu zanga-zanga a kasar Armenia
Masu zanga-zanga a kasar Armenia REUTERS/Vahram Baghdasaryan

Daruruwan Mutane ne suka shiga zanga zanga a Armenia domin tilastawa gwamnatin kasar nemo sojojin da suka bata lokacin da ake fafatawa tsakanin dakarun kasar da na Azerbaijan dangane da rikicin mallakar Nagorno Karabakh.

Talla

Masu zanga zangar da suka hada da fitattun mutane sun yi tattaki a cikin birnin Yereven dauke da hotunan sojojin da suka batan da kuma rubutun dake bukatar dawo da su gida.

Kafin fara tattakin, masu zanga zangar sun karanta budaddiyar wasika ga Jakadan Russia inda suka bukaci ya sanya baki wajen shaidawa gwamnatin sa bukatar ta su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.