Isra'ila

Iran ta kammala jana'izar Fakhrizadeh tare da shan alwashin daukar fansa

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani.
Shugaban kasar Iran Hassan Rohani. © AFP

Bayan kammala jana’izar masanin kimiyyar Iran Mohsen Fakhrizadeh a yau Litinin, wanda kasar ke zargin Isra’ila da kashewa, Iran ta sanar da shirin rubanya ayyukansa baya ga mayar da raddi cikin gaggawa.

Talla

Iran wadda ta bayyana Mohsen Fakhrizadeh a matsayin shahidi, ta ce Isra’ila ce ta yi amfani da wani sabon salo da hadin gwiwar kungiyar MEK da Tehran ta haramta wajen kisan fasihin masanin kimiyyar na ta.

A juma’ar da ta gabata ne, Fakhrizadeh da masu tsaron lafiyarsa suka rasa rayukansu a wani harin bom wanda daga bisani aka bude musu wuta da ya faru a wajen birnin Tehran, harin da Iran ta ce kungiyar ta MEK ce ta kaddamar da shi bisa jagorancin hukumar leken asirin Isra’ila.

Isra’ila dai na kallon Mohsen Fakhrizadeh a matsayin shugaban shirin nukuliyar Iran inda Babban Hafson rundunar tsaron Iran Real-Admiral Ali Shamkani ke cewa harin da ya kashe masanin nukiliyar na cike da sarkakiya, domin babu ko da mahari daya da ya je kan motar Fakhrizadeh yayin farmakin wanda ke nuna an aiwatar da harin ne ta hanyar amfani da fasahar na’ura wajen tayar da bom din da kuma bin su da ruwan harsasai.

Hatta kafafen yada labaran Iran da ke bada bahasin yadda harin ya faru, sun ce ko shakka babu anyi amfani da fasahar bindigu masu sarrafa kansu da aka killace a wani waje na daban yayin farmakin.

A Asabar din da ta gabata ne, Shugaban Iran Hassan Rouhani ya yi zargin cewa Isra’ila ce ta kaddamar da farmakin bisa taimakon Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.