Korea-Amurka

Kim Jung Un ya sha alwashin mallakar karin makaman nukiliya

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un.
Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un. REUTERS/Stringer

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jung Un ya sha alwashin kera karin makaman nukiliya na zamani gami da bayyana Amurka a matsayin babbar abokiyar gaba.

Talla

Kalaman na shugaba Kim na a matsayin gagarumin kalubale ga shugaban Amurka mai jiran gado Joe Biden, yayin da ya rage kwanaki ya karbi ragamar jagorancin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Korea ta Arewa KCNA ya ruwaito shugaba Kim na cewa, munanan manufofin Amurka kansu bai za su canza ba, ko da kuwa an samu sauyin shugabanci a kasar, dan haka yin watsi da manufofin matsawa Korea ta Arewan shi ne kawai matakin da zai gyara alakarsu da Amurkan.

Baya ga makaman nukiliya, Kim Jung Un ya kuma sha alwashin kera karin manyan makamai masu linzami, taurarin dan adam na leken asirin da kuma jirage marasa matuki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.