India-Coronavirus

India ta kaddamar da shirin allurar rigakafin Korona mafi girma a duniya

Wasu ma'aikatan lafiyar kasar India a birnin Mumbai yayin shirin kaddamar da yiwa al'ummar kasar allurar rigakafin cutar Coronavirus. 16/1/2021
Wasu ma'aikatan lafiyar kasar India a birnin Mumbai yayin shirin kaddamar da yiwa al'ummar kasar allurar rigakafin cutar Coronavirus. 16/1/2021 AFP / INDRANIL MUKHERJEE

Gwamnatin India ta kaddamar da soma yiwa al’ummar kasar allurar rigakafin cutar Korona, inda ta fara daga kan ma’aikatan lafiya.

Talla

Hukumomin kasar ta India dai na fatan yiwa mutane miliyan 300 allurar rigakafin cutar ta Korona, kusan adadin daukacin al’ummar Amurka, abinda ya sa shirin zama mafi girma a duniya.

Daga cikin ‘yan Indian miliyan 300 da hukumomin lafiyar kasar ke fatan yiwa allurar rigakafin, akwai kananan yara miliyan 26, likitoci da sauran ma’aikatan lafiya miliyan 30, sai kuma sauran mutane miliyan 270 da shekarunsu suka fara 50 zuwa sama, ko kuma wadanda ke fama da wasu cutukan da ka iya baiwa annobar ta Korona damar tagayyara su.

Yawan al’ummar kasar India ya kai biliyan 1 da kusan miliyan 400, kawo yanzu kuma akalla ‘yan kasar dubu 152 annobar korona ta halaka daga cikin sama da miliyan 10 da suka kamu.

Ranar 4 ga watan Janairu ma’aikatar lafiyar India ta amince da inganci alluran rigakafin da hadin gwiwar jami’ar Oxford da kamfanin AstraZaneca, sai kuma allurar da kamfanin kasar na Bharat Biotech ya samar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.