Iran-Nukilya

Iran ta yi gwajin makamai masu linzami dake cin dogon zango

Yadda dakarun Iran suak yi gwajin makamai masu linzami a wani yankin tsakiyar kasar. 16/1/2021
Yadda dakarun Iran suak yi gwajin makamai masu linzami a wani yankin tsakiyar kasar. 16/1/2021 AFP

Dakarun juyin juya halin Iran sun yi gwajin sabbin jirage marasa matuki da kuma manyan makamai masu linzami dake cikin dogon zango da suka kera a baya bayan nan.

Talla

Dakarun na Iran sun yi gwaje-gwajen ne a akan teku da kuma tudu a ranar Asabar, inda makaman masu linzamin dake cin dogon zango suka yi tafiyar kilomita dubu 1 da 800 akan teku kafin kaiwa ga wurin da aka tsara za su fada a arewacin tekun India.

Karo na 4 kenan da Iran ke atasayen nuna karfin sojinta cikin mako 2, a yayin da dagantaka tayi tsami tsakaninta da gwamnatin Amurka ta shugaba mai barin gado Donald Trump.

Kakakin sojan juyin juya halin na Iran Mohammad Bagheri yace basu da niyyar afkawa wata kasa da yaki, sai dai suna gargadin duk wanda ya takale da cewar za su kaddamar da farmaki kansu da cikakken karfin soji ba tare da bata lokaci ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.