'Yan bindiga sun kashe alkalan kotun kolin Afghanistan 2

Ashraf Ghani, shugaban Afghanistan.
Ashraf Ghani, shugaban Afghanistan. Press Office of President of Afghanistan / AFP

‘Yan bindiga sun bindige wasu mata biyu, alkalan kotun kolin Afghanistan har lahira a wani kwanton baunar da suka musu a babban birnin kasar, Kaboul, a yau Lahadi.

Talla

Mummunan rikici ya kunno kai a sassan Afghanistan a ‘yan watannin bayan nan duk da ci gaba da tattaunawar lalubo zaman lafiya da ake yi tsakanin kungiyar Taliban da gwamnatin kasar, musamman ma a Kabul, inda sabon salon kisan mahimman mutane ke ci gaba da dasa fargaba a zukatan al’umma.

Harin baya bayan nan, wanda manzon Amurka na musamman a Afghanistan, Ross Wilson ya zargi kungiyar Taliban da kaiwa na zuwa ne makonni biyu bayan da ma’aikatar tsaro ta Pentagon ta sanar da rage yawan dakarunta a Afghanistan zuwa dubu 2 da dari 5, mafi karanci a kusan shekaru 20.

Kakakin kotun kolin Afgahnistan, Ahmad Fahim Qaweem ya ce hari kan alkalan ya faru ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa wajen aiki.

Akwai alkalai mata fiye da 200 da ke aiki a kotun kolin Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.