China

China ta musanta zargin gaza daukar matakan dakile Coronavirus

Shugaba Xi Jinping.
Shugaba Xi Jinping. REUTERS/Jason Lee

China ta kare kanta game da matakan da ta dauka don dakile yaduwar Coronavirus tun farkon bullarta cikin watan Disamban 2019, inda ta kalubalanci binciken masana da ke nuna yadda ta yi sakacin barinn cutar ta yadu.

Talla

Rahoton da kwararrun hukumar Lafiya ta Duniya suka fitar yau Talata ya zargi China da gaza daukar matakan da suka dace wajen dakile cutar tun farkon bullarta, zargin da tuni ya karawa Chinar caccaka daga manyan kasashen Duniya wadanda tun farko ke zarginta da kin bayyanawa Duniya halin da ake ciki lokacin da ta fara gano cutar a yankin Wuhan na tsakiyar kasar.

Kwamitin tawagar kwararrun masu binciken wanda WHO ta kafa don gano musabbabin cutar ya ce idan har da China ta dauka matakan gaggawa a farkon bullar cutar ko shakka babu bazata basu zuwa sassan Duniya tare da yin bannar da ta yi ba.

Sai dai a martanin da ta mayar, Chinan ta ce babu gaskiya a batun da ke cewa bata dauki matakan da suka kamata ba, amma a shirye ta ke ta kara kaimi wajen yaki da cutar wadda zuwa yanzu ta hallaka mutane miliyan biyu da dubu dari 3 a sassan Duniya.

A cewar ministan harkokin wajen China Hua Chunying, Beijing ta sanya tsauraran matakan da suka hana cutar tasiri a cikin kasar amma abin takaici ta yi gagarumar barna kama daga ta rai da kuma tattalin arziki a kasashen Duniya.

Chunying ya sanar da cewa tun a wancan lokaci China ta sanya dokar takaita walwala baya ga kulle yankunan da aka samu bullar cutar don hana ta bazuwa, wanda kuma ya taimaka matuka, batun da a cewarsa yakamata ya ankarar da sauran kasashe don daukar matakan da suka kamata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.