Iraqi

Harin kunar bakin wake ya ragargaza wani sashin kasuwar birnin Bagadaza

Sashin kasuwar birnin Bagadaza da ya fuskanci harin kunar bakin wake.
Sashin kasuwar birnin Bagadaza da ya fuskanci harin kunar bakin wake. Reuters

Harin kunar bakin wake da safiyar yau Alhamis ya halaka mutane da dama tare da jikkata gwammai a wata kasuwa dake tsakiyar Bagadaza, babban birnin kasar Iraqi.

Talla

Bayanai sun ce akalla mutane 28 suka mutu a harin, yayin da wasu sama da 25 suka jikkata, kamar yadda wasu jami’an ‘yan sanda da suka nemi sakaya sunansu suka bayyana.

Jami’an tsaron sun yi gargadin cewa adadin mutanen da suka mutu a kasuwar ta birnin Bagadaza ka iya karuwa.

Rabon da a kai irin wannan hari a babban birnin na Iraqi dai tun watan Yunin shekarar 2019, inda mutane da dama suka halaka.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, wanda yayi kama da na kungiyar IS, wadda hukumomin tsaron kasar da kawancen Amurka suka yi shelar murkushe ta a shekarar 2017, bayan gwabza kazamin yaki da ita tsawon shekaru 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.