sama da mutane 30 sun mutu sakamakon harin kunar bakin wake a kasuwar Iraqi

Jami'an tsaron Iraqi yayin tabbatar da tsaro a yankin kasuwar birnin Bagadaza da aka kaiwa harin kunar bakin wake
Jami'an tsaron Iraqi yayin tabbatar da tsaro a yankin kasuwar birnin Bagadaza da aka kaiwa harin kunar bakin wake Reuters

Wasu tagwayen hare – hare da ba a saba gani ba a birnin Bagadaza ya yi sanadin mutuwar mutane 32 tare da jikkata sama da 100 a wani kasuwa mai cinkoson jama’a, kamar yadda kafofin yda labarin Iraqi suka ruwaito.

Talla

Harin wanda shi ne mafi muni a cikin shekaru 3 da suka gabata, ya rutsa da mutane da dama da ke hada hada a bangaren ‘ya gwanjo na babban kasuwar Bagadaza.

Kasuwar na samun halartar dimbim masu cinta  tun da aka sake bude ta, bayan kusan shekara guda da takaita zirga –zirga da taron jama’a a kasar da hukumomi suka yi da zummar dakile yaduwar annobar corona.

A cewar wata sanarwa daga ma’ikatar cikin gida ta kasar, dan kunar bakin waken na farko ya shiga kasuwar a gigice ne yana ikirari rashin lafiya tare da neman dauki, bayan mutane sun taru a kan sa ne ya tada bam din da ke jikinsa, ana cikin ribibi ne maharin na 2 ya tada nasa.

Harin shine mafi muni tun bayan na watan Janairun 2018, lokacin da wani dan kunar bakin wake ya kashe mutane 30 a wannan wuri.

Fafaroma Francis, wanda ke fatan ziyartar Bagadaza a watan Maris mai zuwa ya yi Allah wadai da harin wanda ya kira ‘tsabagen mugunta da rashin hankali’.

Shugaba Burham Saleh na Iraqi shi ma ya jagoranci kusoshin siyasar kasar wajen yin tir da harin, yana mai cewa gwamnati za ta yi tsayuwar gwamin jaki wajen taka wa bata - gari masu neman wargaza kasar birki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.