China

China ta ceto masu hakar ma'adanai 11 bayan shafe makonni 2 makale a rami

Jami'an agaji a China dake ceto masu hakar ma'adanai
Jami'an agaji a China dake ceto masu hakar ma'adanai Reuters

Jami’an agaji a China sun samu nasarar ceto mutane 11 daga cikin masu hakar ma’adanai 22 da suka shafe akalla makwanni 2 makale a ramin da suke aiki, dake gabashin kasar.

Talla

Gidan talabijin dan kasar China ta nuno yadda aka ceto mutun na farko cikin ramin sanya da bakin Kellen baiwa ido kariya da sanyin safiyar yau.

Bayanai sun ce an gano mutum na farko da aka ceto ne shi kadai a wani bangaren ramin hakar ma’adanan.

Tun ranar 10 ga watan Janairun da muke ciki, mahakan ke makale a ramin hakar ma’adanai na Hushan mai zurfin daruruwan mitoci dake lardin Shandong.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.