Iran-Isra'ila

Isra'ila na shirin kai wa Iran hari don hana ta mallakar Nukiliya

Wasu jiragen yakin Isra'ila yayin atisaye.
Wasu jiragen yakin Isra'ila yayin atisaye. CHRISTOF STACHE / AFP

Shugaban Sojin Isra'ila Janar Aviv Kochavi ya ce ya bada umurnin tsara shirin kai wa kasar Iran hari domin hana ta cigaba da shirin mallakar makamın nukiliya.

Talla

Janar Kochavi ya ce ya umurci kwamnadodin sa da su shirya tsari daban-daban akan wadanda su ke da shi, duk da ya ke shugabannin siyasar kasar ne kawai ke da hurumin bada umurnin kai mata hari.

Shugaban sojin ya soki yarjejeniyar nukiliyar da Iran ta kulla da kasashen duniya, wanda ya kunshi Amurka a ciki, kafin janye kasar da tsohon shugaba Donald Trump yayi.

Kochavi ya ce dole a ci gaba da matsawa Iran lamba wajen ganin ba’a bata damar mallakar makamin Nukiliyar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.