Myanmar-Rohingya

'Yan kabilar Rohingya na murnar hambarar da gwamnatin Myanmar

Wasu 'yan gudun hijirar kabilar Rohingya a Bangladesh.
Wasu 'yan gudun hijirar kabilar Rohingya a Bangladesh. REUTERS/Rafiqur Rahman

'Yan Kabilar Rohingya Musulmi da suka samu mafaka a kasar Bangladesh sakamakon azabar da suka sha a hannun sojin Myanmar shekaru 3 da suka gabata, sun bayyana farin cikin su da juyin mulkin da aka yiwa Aung San Suu Kyi da kuma tsare ta.

Talla

Akalla 'an Kabilar Rohingya dubu 740 suka tsere daga Myanmar zuwa Bangladesh a shekarar 2017 domin samun mafaka a hare haren da aka kai musu wanda Majalisar Dinkin Duniya ta ce na iya zama laifuffukan yaki.

Farid Ulla, daya daga cikin shugabannin al’ummar Rohingya mazauna Katupalong, sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a Bangladesh ya ce Suu Kyi ce silar halin kuncin da suka samu kan su, saboda haka ya zama wajibi su bayyana farin cikin su da halin da ta shiga.

Mohammed Yusuf, wani shugaba a sansanin Balukhali, ya ce dama ita ce fatar su ta karshe, amma sai ta yi watsi da bukatun su lokacin da ta karbi ragamar iko.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewar wasu 'yan kabilar ta Rohingya sun gudanar da addu’oi domin godewa Allah kan abinda ya faru a Myanmar wanda suka bayyana a matsayin ramako a gare su.

Maung Kyaw Min, mai Magana da yawun kungiyar daliban Rohingya, ya ce sakamakon abinda ya faru suna da fatar cewar za su samu damar komawa kasar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI