Falasdinu

Hamas da Fatah da basa ga maciji da juna na shirin ganawa don tinkarar zaben kasar

Shugaban tawagar Hamas Saleh Arouri da na Fatah Azzam Ahmad yayin rattaba hannu kan yarjejeniar sulhu da juna a Alkhahiran Masar 12, 2017.
Shugaban tawagar Hamas Saleh Arouri da na Fatah Azzam Ahmad yayin rattaba hannu kan yarjejeniar sulhu da juna a Alkhahiran Masar 12, 2017. REUTERS/Amr Abdallah Dalsh

Kungiyoyin Falasdinawa biyu da suka hada da Fatah mai iko da Gabar Yamma da Kogin Jordan, da Hamas dake iko da Gaza, sun bayyana shirin gudanar da wani taro a birnin Alkahira wannan makon domin tattauna matsalolin dake yiwa shirin zaben su barazana.

Talla

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya sanya ranar 22 ga watan Mayu mai zuwa a matsayin ranar zaben 'Yan Majalisu, yayin da za’a gudanar da zaben shugaban kasa ranar 31 ga watan Yuli, kuma shine irin sa na farko tun wanda akayi a shekarar 2006.

Zaben baya da akayi ya nuna yadda kungiyar Hamas ta samu gagarumar rinjaye a zaben 'Yan Majalisu, sakamakon da Fatah taki amincewa da shi.

Masana na cewa rashin hadin kan bangarorin biyu na daga cikin matsalolin dake dakushe kimar fafutukar da suke yin a kafa kasar Falasdinu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI