Iran-Nukilya

Hukumar sa ido kan nukiliya ta fara tattaunawa da Iran

Shugaban Iran Hassan Rohani,
Shugaban Iran Hassan Rohani, REUTERS/Brendan McDermid

Shugaban hukumar sa ido kan makamshin nukuliya ta majalisar dinkin duniya, Rafael Grossi ya soma tattaunawa da shugabannin Iran kan shirinta na nukiliya, sa’o’i gabannin cikar wa’adin da ta diba na takaita bincike daga hukumar idan Amurka ba ta dage takukuman da t kakaba mata ba.

Talla

Ziyarar na zuwa a yayin da Amurka da Tarayyar Turai suka kara azama a kokarinsu na ceto yarjejeniyar nukiliyar 2015, wacce ke daf da rugujewa tun bayan da tsohon shugaba Donald Trump ya jaanye daga cikinta.

Muddin wa’adin ya cika ba tare da Amurka ta janye takunkuman ba, Iran za ta kara bijirewa yarjejeniyar ta da manyan kasashe kan shirin ta na nukiliya.

A daren jiya Asabar ne shugaban hukumar sa ido a kan makamashin nukiliyar ya sauka birnin Tehran, ya kuma gana da shugaban hukumar makamashin nukiliyar Iran Ali Akbar Salehi da sanyin safiyar Lahadi, kamar yadda kafar talabijin kasar ta nuna.

Ministan harkokin wajenn Iran Javad Zarif ya shaida wa kafar talabijin na Press TV cewa anjima a Lahadin nan zai gana da Mr. Grossi.

Iran ta sha nanata cewa za ta cika alkawurran da ta dauka a bisa yarjejeniyar nukiliyar muddin Amurka ta janye takunkuman karayar tattalin arziki da ta kakaba mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI