Iran-Nukiliya

Hukumar IAEA ta nuna damuwa kan gano sinadaran Nukiliya a Iran

Rafael Mariano shugaban hukumar da ke sanya idanu kan makaman Nukiliya ta Majalisar dinkin Duniya.
Rafael Mariano shugaban hukumar da ke sanya idanu kan makaman Nukiliya ta Majalisar dinkin Duniya. JOE KLAMAR / AFP

Hukumar yaki da yaduwar makaman nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana matukar damuwa kan samun sinadarin hada makamin nukiliya a wani wuri da kasar Iran bata gabatar mata ba.

Talla

Rahotan da kungiyar ta rubuta wanda kamfanin dillancin labaran Faransa ya gani ya nuna rashin dadin sa da samun wannan sinadarin a wurin da bata san da zaman sa ba.

Rahotan ya ce bayan watanni 18 Iran ta gaza wajen gabatar mata da bayanai masu sahihanci da za ta amince da su dangane da samun sinadarin.

Shi dai wannan wurin da aka gano yana yankin Turquzabad ne a Tehran, wanda Isra'ila ta sanar da gano shi a matsayin wanda ake aiki a ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI