Malaysia-Myanmar

Malaysia ta tisa keyar 'yan ciranin Myanmar fiye da dubu 1 zuwa gida

Wasu 'yan ciranin Myanmar.
Wasu 'yan ciranin Myanmar. REUTERS/Stringer

Malaysia ta mayar da ‘yan ciranin Myanmar fiye da dubu guda da ta ke tsare da su zuwa kasarsu yau Talata, duk da umarnin Kotu da ya hana mayar da su kasar ta su wadda ta fuskanci juyin mulkin Soji makwanni 2 da suka gabata.

Talla

Shirin mayar da ‘yan ciranin fiye da dubu guda, ya gamu da caccaka daga kungiyoyin kare hakkin dan adam, wanda ya kai ga mika batun gaban kotu wadda ta dakatar da shi.

Bayanai sun ce an fara aikin kwashe ‘yan ciranin a manyan motocin daukar kaya da na fasinja baya ga safa-safa, gabanin a dura su a manyan jiragen Sojin Ruwan Myanmar 3 da suka tsaya a gabar ruwan kasashen biyu.

Tuni dai kasashen Amurka da Majalisar Dinkin Duniya suka caccaki matakin gwamnatin Malaysia inda suka ce kaso mai yawa na ‘yan ciranin da kasar ta tisa keyarsu zuwa Myanmar masu neman mafaka ne da suka tsere daga kasashensu.

Sa’o’i kalilan gabanin fara aikin mayar da ‘yan ciranin, sai da babbar kotun Kuala Lumpur ta dakatar da yunkurin na gwamnati bisa kafa hujja da cewa matukar Malaysian ta aiwatar da shirin ko shakka babu ta sabawa dokokin kasa da kasa musamman ganin yadda mulki ke hannun Soji yanzu haka a kasar ta Myanmar, batun da ke nuna rayuwar masu neman mafaka a cikin ‘yan ciranin na cikin hadari.

Tuni dai jiragen suka tafi da ‘yan ciranin dubu 1 da 86 ba tare da mahukuntan Malaysia sun yiwa kotu bayani kan dalilin da ya sanya su bijirewa umarninta ba.

Sai dai shugaban hukumar shige-da-fice na Malaysia Khairul Dzaimee Daud ya bayyana cewa babu ko da mutum guda ‘yan kabilar Rohingya ko kuma masu neman mafaka da ke cikin ‘yan ciranin da aka dora a jirgin don mayar da su gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI