Myanmar-Arangama

Magoya bayan sojoji sun yi arangama da masoyan Suu Kyi a Myanmar

Magoya bayan sojoji  sun yi arangama masoyan Aung San Suu Kyi a birnin Yangon na Myanmar
Magoya bayan sojoji sun yi arangama masoyan Aung San Suu Kyi a birnin Yangon na Myanmar Ye Aung Thu AFP

Magoya bayan sojin da suka yi juyin mulki a Myanmar sun yi arangama da masu adawa da kifar da gwamnatin Aung San Suu Kyi a babban birnin Yangon, yayin da hukumomi suka dakile dalibai a makarantunsu don hana su zanga-zanga a wannan Alhamis.

Talla

Tun lokacin da sojoji suka yi juyin mulki a ranar 1 ga watan Fabairu tare da tsare Suu Kyi, kasar ta tsunduma cikin tashin hankali.

Kimanin makwanni uku kenan da ake gudanar da zanga-zanga a kowacce rana da kuma yajin aiki a kasar, kuma dalibai sun lashi takobin sake yin dandazo a babban birnin Yangon a yau Alhamis.

Sai dai ‘yan sanda sun rufe kofofin  makarantunsu don hana darruruwan daliban fitowar dango.

Duk da cewa, an hana daliban fitowa, amma an samu hatsaniya tsakanin magoya bayan sojoji da kuma magoya bayan Suu Kyi, inda rahotanni ke cewa, an samu raunuka.

Magoya bayan sojojin da adadinsu ya kai dubu 1 sun yi barazana hatta ga ‘yan jarida da  masu daukar hoto, yayin da suka yi ta cilla duwatsu da kuma harba gwafa kamar yadda shaidu suka tabbatar.

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI