Yemen - Huthi

Farmaki tsakanin 'yan tawaye da dakarun Yemen ya hallaka mayaka 60

Tankar yaki a kasar Yemen, yayin fafatwa tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye
Tankar yaki a kasar Yemen, yayin fafatwa tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye Nabil HASAN AFP/File

Mayaka fiye da 60 aka kashe a kasar Yemen bayan fafatawa tsakanin 'yan tawayen Huthi da ke samun goyon bayan Iran da sojojin gwamnati a lardin Marib da ke arewacin kasar.

Talla

Majiyar gwamnatin kasar Yemen ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, akalla sojoji gwamnati 27 da ‘yan tawayen Huthi 34, aka kashe  a gumurzun na Yau Jumma’a .

A cewar majaliyar wannan farmakin shine mafi muni, tun bayan sake barkewar rikici a ranar 8 ga watan nan na Fabarairu, lokacin da 'yan tawayen Huthi dake samun goyan bayan Iran suka kara kaimi don kwace iko da garin Marib, mai nisan kilomita 120 gabas da Sanaa babban birnin da dama can ke hannun su.

Garin na kusa da wasu mahimman wuraren hakar mai ne, a Yemen, kuma kame shi zai kasance babbar nasara ga 'yan tawayen.

Majiyar tace, 'Yan tawayen sun haura saman kan tsaunuka kusa da wata madatsar ruwa da ke kudu maso yammacin garin na Marib da yanzu haka ke matsayin tungan karshe a arewaci ga dakarun gwamnati dake samun goyan bayan Saudiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.