Myanmar

Jakadan Myanmar a MDD ya bukaci kawo karshen juyin mulkin soji a kasar sa

Jakadan Myanmar a Majalisar Dinkin Duniya Kyaw Moe Tun, yayin da yake jawabin neman kawo karshen juyin mulkin soji a kasar sa a gaban Majalisar
Jakadan Myanmar a Majalisar Dinkin Duniya Kyaw Moe Tun, yayin da yake jawabin neman kawo karshen juyin mulkin soji a kasar sa a gaban Majalisar Via REUTERS - United Nations TV

Jakadan Myanmar a Majalisar Dinkin Duniya Kyaw Moe Tun, ya yi kira da a gaggauta kawo karshen juyin mulkin da sojoji sukayi a kasar tare da kira ga kasashen duniya da su tashi tsaya kan wannan batu. 

Talla

Moe wanda ke jawabi ga taron Majalisar Dinkin Duniya, ya kuma nuna goyan bayan sa ga masu zanga-zangar neman sakin hambarerriyar jagorar yankin Aung Sang Suu kyi da kuma maida mata mulki, inda ya daga yatsun sa uku, dake nuna alaman goyon bayan.

Jami'in diflomasiyyar ya ce

"Muna bukatar daukar kwakwarar mataki daga kasashen duniya don gaggauta kawo karshen juyin mulkin da sojoji suka yi, da danniyar mutanen da ba su ji ba su gani ba, sannan a maido da gwamnatin da jama'a ta amince"

Takaiceccen jawabin nasa cikin yanayin tausayi, ya samu goyon bayan takwararorinsa a zauren Majalisar da suka jinjina masa, kamar wakilin Tarayyar Turai, Olof Skoog da Jakadiyar Burtaniya a Majalisar Barbara Woodward.

Kyaw Moe Tun ya bukaci membobin Majalisar Dinkin Duniya da kar su amince da kuma ba da hadin kai ga gwamnatin soja da ta kwace mulki a ranar 1 ga Fabrairu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.