Myanmar

Zanga-zangar adawa da juyin mulkin sojoji a Myanmar na neman kazancewa

Jami'an tsaron Myanmar cikin shirin ko ta kwana bayan murkushe yunkurin masu zanga-zanga na sake taruwa. 27/2/2021.
Jami'an tsaron Myanmar cikin shirin ko ta kwana bayan murkushe yunkurin masu zanga-zanga na sake taruwa. 27/2/2021. AP - STR

Jami'an tsaron Myanmar sun murkushe yunkurin masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi na sake taruwa, lamarin da ya janyo arrangamar da ta kai ga mutuwar wata mata, da 'yan sanda suka harbe har lahira.

Talla

A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan Myanmar ta baza dubban jami’an ta zuwa yankuna da dama, musamman Yangon babban birnin kasar, inda suke sintiri a wuraren da masu zanga-zanga suka saba taruwa.

Dubban ‘yan kasar ta Myanmar dai sun shafe sama da makwanni biyu suna zanga-zangar adawa da kifar da gwamnatin Aung San Su Kyii, bayan da sojojin kasar suka ce an tafka magudi a zaben da ya gudana na watan Nuwamba, wanda jam’iyyar hambararriyar shugabar NLD ta lashe da gagarumin rinjaye.

Har yanzu dai babu tabbas kan halin da Su Kyii ke ciki, tun bayan da sojoji suka tsare ta tare da wasu na hannun damanta, yayin juyin mulkin da suka aiwatar a ranar 1 ga watan Fabarairu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI