Zanga-zangar - Mynamnar

Majalisar Dinkin Duniya da EU sun yi tir da murkushe masu zanga-zanga a Myanmar

Sojojin Myanmar dake kokarin murkushe masu zanga-zangar a kasar
Sojojin Myanmar dake kokarin murkushe masu zanga-zangar a kasar REUTERS - STRINGER

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Tarayyar Turai sunyi Allah wadai da matakin shugabannin sojin Myanmar na murkushe masu zanga-zangar luma, tare da bukatar ganin an daina amfani da karfin da ya wuce kima a kansu.

Talla

Cikin wata sanarwa Kakakin Hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Ravina Shamdasani tayi tir da matakin bayan da sojoji sukayi amfani da karfin da ya wuce kima kan masu zanga-zangar neman kawo karshen juyin Mulki.

Yayin da shugaban diflomasiyar Turai Josep Borrell yayi tir da matakin Gwamnatin mulkin sojan kasar da ke kokarin shawo kan dandazon mutane da ke mamaye tituna don neman mika Mulki ga fararen hula da kuma sakin jagoran yankin Aung San Suu Kyi, wacce aka tsare tare da manyan makarrabanta na siyasa.

Embed: Shugaban diflomasiyar Tarayyar Turai ya yi tir da murkushe masu zanga-zanga a Myanmar

Rahatanni na cewa, jami'an tsaron Myanmar sun bude wuta kan fararen hula, tare da kashe mutane da dama, wanda ke amatsayin mafi muni da aka taba gani, a kokarin da ake na murkushe masu adawa da juyin mulkin na tsawon makonni hudu.

Wannan na zuwa ne bayan da Gwamnatin sojin Myanmar ta kori jakadan kasar a Majalisar Dinkin Duniya daga mukaminsa, bayan da yayi alla-wadai da yadda suke yin amfani da karfi wajen murkushe masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin da suka yin a kifar da gwamnatin Aung San Su Kyii.

Yayin caccakar sojin na Myanmar tsohon jakadan Kyaw Moe ya bukaci al’ummar Myanmar da su cigaba da zanga-zanga har sai burinsu ya cika na kawar da gwamnatin sojin da suka yi juyin mulki a ranar 1 ga watan nan na Fabarairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.