Myanmar-Majalisar Dinkin Duniya

Dubban 'yan Myanmar sun yi tsayuwar gwamen jaki kan aniyar korar gwamnatin soja

Masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Myanmar.
Masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Myanmar. AP - STR

Dubban masu zanga-zanga sun sake fantsama kan tituna a Myanmar kwana guda bayan kashe mutane sama da 50 da jami’an tsaro suka yi, a cigaba da kokarin murkushe zanga-zangar adawa da juyi mulkin da sojoji suka yi.

Talla

Larabar da ta gabata ce rana mafi muni ga masu zanga-zanga a Myanmar, bayan da fararen hula akalla 38 suka mutu yayin arrangama da jami’an tsaron dake kokarin murkushe su, kamar yadda alkaluman majalisar dinkin duniya  suka nuna, adadi mafi yawa tun bayan soma boren adawa da kifar da gwamnatin tsohuwar shugaba Aung San Su Kyii da sojojin kasar suka yi a ranar 1 ga watan Fabarairun da ya gabata.

Shugabar hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya Michelle Bachelet wadda ta yi tirr da yadda jami’an tsaron Myanmar ke bude wuta kan masu zanga-zanga, ta bukaci gaggauta dakatar da kisan gillar da suke yiwa fararen hula tare da garkame daruruwansu a gidajen Yari.

Alkaluman baya bayan nan da hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya ta fitar sun nuna cewar akalla mutane 54 suka rasa rayukansu a Myanmar tun bayan soma zanga-zangar adawa da juyin mulkin da sojojin kasar suka yi.

Yanzu haka dai masu boren sun sake mamaye titunan Yangon da Mandalay, birane biyu mafiya girma a kasar ta Myanmar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.