China

China za ta kara kasafin bangaren tsaro saboda rikicinta da Amurka

Zaman Majalisar Sojin China.
Zaman Majalisar Sojin China. AP - Andy Wong

Hukumomin Kasar China sun bayyana cewar za a kara kasafin kudin kasar da ke kula da bangaren soji da kashi kusan 7 a cikin wannan shekarar, sakamakon tankiyar da kasar ta ke samu tsakanin ta da wasu kasashen duniya irin su Amurka da India akan yankin Himalaya da Taiwan da tekun da ke kudancin kasar.

Talla

Ma’aikatar kudin China ta ce za ta kashe Dala biliyan 210 akan harkokin tsaro, kasafin da ke nuna kasa da kashi guda bisa uku na sojin Amurka a wannan shekarar.

A shekarun da suka gabata, China tayi ta zuba triliyoyin kudin kasar na Yuan wajen sabunta kayanta na soji da kuma kera sabbin makamai domin samarwa kan ta tsaron da ya dace.

Yanzu dai haka China ce ta biyu bayan Amurka wajen kashe kudi akan harkokin soji.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.