Saudiya-Houthi

Mayakan Houthi sun harba makamai masu linzami 8 kan Saudiya

Wani makami mai linzami kirar kasar Iran da hukumomin tsaron Saudiya suka harbo, bayan yunkurin kaiwa filayen hakar manta farmaki da mayakan Houthi suka yi.
Wani makami mai linzami kirar kasar Iran da hukumomin tsaron Saudiya suka harbo, bayan yunkurin kaiwa filayen hakar manta farmaki da mayakan Houthi suka yi. AP - Amr Nabil

Mayakan ‘yan tawayen Houthi dake Yemen sun sanar da harba makamai masu linzami 8 da kuma jirage marasa matuka 14 da zummar kai farmaki kan kayayyakin kamfanin hakar man Saudiya na Aramco da kuma wasu sansanonin sojin kasar.

Talla

Cikin sanarwar da suka fitar ta hannun kakakinsu Yahya Sarea ‘yan tawayen na Houthi sun ce wuraren da suka kaiwa farmakin na sassan biranen Dammam, Asir da kuma Jazan.

Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan labari, hukumomin tsaron Saudiya basu ce komai kan ikirarin mayakan na Houthi ba.

A baya bayan nan dai, mayakan Houthi sun matsa wajen kokarin kaiwa wasu biranen Saudiya farmaki da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuki, said ai hakarsu ta gaza cimma ruwa, sakamakon kakkabo makaman da hukumomin tsaron kasar ta saudiya ke yi.

Wasu mayakan 'yan tawayen Houthi a birnin Sanaa na kasar Yemen.
Wasu mayakan 'yan tawayen Houthi a birnin Sanaa na kasar Yemen. AP - Hani Mohammed

Kafin harin na baya bayan nan, rundunar sojin Saudiya ta sanar da kaiwa wasu sansanonin mayakan na Houthi farmaki a birnin San’a da wasu sassan kasar Yemen a cigaba da kokarin kasar ta Saudiya wajen murkushe tawayen da mayakan suka share shekaru suna yi.

A ranar Asabar 6 ga watan Maris,  rundunar sojin Yemen ta ce mayaka akalla 90 ne suka rasa rayukansu yayin gumurzun da dakarunta suka da ‘yan tawayen Houthi cikin sa’o’i 24 a birnin Marib.

Mayakan na Houthi dai sun shafe makwanni sun kokarin kwace iko da birnin Ma’arib, wanda rasa shi zai zama babban koma baya ga gwamnatin Yemen dake samun goyon bayan dakarun kasar Saudiya dake jagorantar sauran sojojin kawance.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.