Syria-Coronavirus

Shugaban Syria Bashar al-Assad da mai dakinsa sun kamu da coronavirus

Syria's President Bashar al-Assad speaks during an interview with Russia's RIA news agency, in Damascus, Syria in this handout picture provided by SANA on March 30, 2016.
Syria's President Bashar al-Assad speaks during an interview with Russia's RIA news agency, in Damascus, Syria in this handout picture provided by SANA on March 30, 2016. REUTERS/SANA/Handout via Reuters

Shugaba Bashar al-Assad na Syria da mai dakinsa Asma Assad sun kamu da cutar Coronavirus bayan wani gwaji a yammacin jiya Litinin, dai dai lokacin da cutar ke ci gaba da tsananta a sassan kasar.

Talla

Fadar shugaban kasar da ke tabbatar da kamuwar Bashar al-Assad, ta ce tun farko shugaban mai shekaru 55 da mai dakinsa sun fara nuna alamomin cutar ne wanda ya kai ga yi musu gwaji.

Sanarwar fadar ta ce shugaban da iyalinsa za su killace kansu na akalla makwanni 3 don ganin abin da hali zai yi, duk da cewa yanzu haka suna cikin koshin lafiya.

Kamuwar Assad da Coronavirus na zuwa makwanni bayan kasar ta fara rigakafin Coronavirus kan jami’an Lafiya da nau’in rigakafin da ta karba daga kawarta wadda ba ta bayyana ko wacce kasa ba ce.

Cutar korona a Syria

Zuwa yanzu Syria na da alkaluman mutum dubu 15 da 981 wadanda suka harbu da Coronavirus, ciki har da dubu 1 da 63 da cutar ta kashe, yayinda yankin da ke hannun Kurdawa ya sanar da samun mutum dubu 8 da 689 masu cutar sai wadanda ta kashe 368 a bangare guda kuma yankin da ke hannun ‘yan tawaye ya sanar da samun masu dauke da cutar dubu 21 da 209 ciki har da matattu 632.

Wata majiya ta daban ta ce mukarraban gwamnati na gab da karbar nasu rigakafin allurar ta coronavirus cikin alluran da za su isa kasar a karshen watan nan karkashin shirin Covax.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.