China-Hong Kong

China ta kafa dokar zabawa yankin Hong Kong 'yan takara

Dubban masu zanga-zangar adawa da tasirin mulkin China a yankin Hong Kong.
Dubban masu zanga-zangar adawa da tasirin mulkin China a yankin Hong Kong. AP - Gemunu Amarasinghe

Majalisar dokokin China, ta kada kuri’ar amincewa da dokar sauya tsarin zaben yankin Hong Kong, ciki har da baiwa kasar damar tantance ‘yan takarar da suka cancanci tsayawa takara a zabukan yankin.

Talla

Dan majalisa daya ne tak daga cikin dubu 2 da 896, ya kauracewa jefa kuri’ar amincewa da dokar sauya tsarin zaben na Hong Kong, domin tabbatar da cewa wadanda ke biyayya ga gwamnatin China ne kawai za a baiwa damar jagorantar yankin.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da China ke kakabawa Hong Kong doka mai tsanani ba, domin a shekarar bara ta kafawa yankin dokar tsaron da ta tsananta hukunci kan masu batanci ga gwamnatin kasar ta China.

Matakin China na cigaba da takaita tsarin Dimokaradiyyar Hong Kong dai ya biyo bayan zanga-zangar da dubban masu goyon bayan komawa bin tsarin dimokaradiyyar Turai da ta kazance a shekarar 2019.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.