Japan-Tsunami

Japan na makokin cika shekara 10 da afkuwar girgizar kasar Tsunami

Wasu al'ummar Japan yayin shirin 'yan mintuna yau Alhamis 11 ga watan Maris na 2021 lokacin cika shekaru 10 dai dai da girgizar kasar Tsunami da kasar ta gani a 2011.
Wasu al'ummar Japan yayin shirin 'yan mintuna yau Alhamis 11 ga watan Maris na 2021 lokacin cika shekaru 10 dai dai da girgizar kasar Tsunami da kasar ta gani a 2011. REUTERS - KYODO

Al’ummar Japan na makokin cika shekaru 10 da rasa rayukan dubunnan ‘yan kasar da mummunar girgizar Tsunami ta kasar 2011 ta shafa, girgizar kasar da ta kai ga fashewar tashar nukiliya wanda ya hallaka mutane kusan dubu 20.

Talla

Al’ummar kasar ta Japan sun yi shirun mintuna wanda ya fara daga karfe 2 da minti 46 na tsakar ranar yau, wato kwatankwacin dai dai lokacin da hirgizar kasar ta faro daga yankin arewa maso gabashin kasar a ranar 11 ga watan maris na 2011.

Akalla mutum dubu 18 da 500 aka tabbatar da sun rasa rayukansu a girgizar kasar ta Tsunami mai karfin maki 9 hade da fashewar tashar Nukiliya ta Fukushima wadda aka bayyana da na mafi munin ibtila'i da Japan ta gani a tarihi.

Da ya ke bayani gaban taron makokin, sarkin gargajiyar Japan Naruhito, ya ce ibtila’in lamari ne da kasar ba za ta taba mantawa da shi ba,  yayinda har yanzu wasu da ibtila’in ya shafa musamman mazauna yankunan gab da tashar Nukiliyar ta Fukushima s uke ci gaba da jin jiki game da illar da fashewar tashar ya yi musu.

Taron makokin wanda ya gudana a babban dakin taro na Tokyo, ya samu halartar jiga-jigan mahukuntan kasar da kuma wadanda ibtila’in na wancan lokaci ya kassara,   

Firaministan Japan Yoshihide Suga ya ce kalubalen da wadanda suka tsira da rayukansu daga Ibtila’in su ke ya karu bayan bullar annobar Coronavirus da kuma girgizar kasar baya-bayan nan da yankin ya fuskanta.

Tun a wancan lokacin dai malalar fashewar tashar nukiliyar ta Fukushima ne ya tarad da yankunan gefen inda tashar ta ke wanda ya hade da girgizar kasa tare da haddasa gagarumar ta’asa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.