Myanmar-Arangama

Masu zanga-zanga sun ci gaba da bijire wa hukumomin soji a Myanmar

Masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin Myanmar a birnin yangon.
Masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin Myanmar a birnin yangon. REUTERS - STRINGER

Akalla mutum guda ya mutu a ranar Lahadi a yayin da masu zanga-zangar adawa da juyin mulki a kasar Myanmar ke ci gaba da biijire wa mulkin soji, kwana guda bayan da ‘yan majalisar dokokin da aka wancakalal, wadanda a yanzu haka suke buya, suka nuna goyon bayansu a garesu.

Talla

 Myanmar ta kasance cikin tashin hankali tun da sojoji suka hambarar da jagorar farar hular kasar, Aung San Suu Kyi daga kan mulki a ranar 1 ga watan Fabrairu, lamarin da ya tunzura dubun dubatan ‘yan kasar gudanar da zanga-zangar neman ceto dimokaradiyya.

Sojojin da suka yi juyin mulkin sun sha nanata hujjar kwace mulki, inda suke zargin an tafka magudi a zabukan watan Nuwamban 2020, wanda jam’iyyar Suu Kyi ta National League for Democracy ta samu gagarumar nasara.

A martaninsu, wata kunggiyar hambararrun ‘yan majalisar dokokin kasar, wadanda da dama daga cikinsu suke buya, sun kafa wata “majalisar  boye” da zummar turje wa sojoji masu juyin mulkin.

Fiye da mutane 80 ne suka mutu a tashe-tashen hankula da suka biyo bayan juyin mulkin.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.