Iraqi

Fitaccen dan safarar kwayoyi ya kubce daga hannun jami'an tsaron Iraqi

Wasu jami'an tsaron Iraqi yayin aikin sintiri.
Wasu jami'an tsaron Iraqi yayin aikin sintiri. Reuters/路透社

Wasu Sojin gona a Iraqi sun yi nasarar kubutar da wani fitaccen mai safarar miyagun kwayoyi da aka kama jiya Lahadi dauke da hajjar sa lokacin da ake hanyar kai shi kotu yau Litinin domin fuskantar tuhuma a kotun da ke Amara, babban birnin Yankin.

Talla

‘Yan sanda sun ce akalla jami’an su 100 ne ke rakiyar wanda ake zargi, lokacin da wasu sanye da kayan soji suka tare su a hanya, suka kuma karbe shi daga hannun su kafin su gudu da shi.

Wata majiyar 'yan sanda ta ce 'yan bindigar na samun goyan bayan wasu fitattun mutane ne wadanda yaki bayyana sunan su saboda dalilan tsaro.

Yankin Missan da ke kudancin kasar Iraqi ya yi kaurin suna wajen yawan masu safarar miyagun kwayoyi da ke samun goyan bayan wasu kungiyoyin Iran da ke iko da yankin.

Lokacin mulkin Saddam Hussein amfani da miyagun kwayoyi na dauke da hukuncin kisa, amma bayan kawar da shi an samu karuwar masu safara da shan sa, yayin da ake amfani da kasar wajen kai shi Turai daga Afghanistan da Iran.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.