Myanmar

Karin masu zanga-zanga 18 sun mutu a Myanmar

Dubban masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin da sojojin Myanmar suka yi.
Dubban masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin da sojojin Myanmar suka yi. © REUTERS/Stringer

Masu zanga-zangar kin jinin juyin mulkin sojoji a Myanmar akalla 18 aka kashe, wasu kimanin 50 suka jikkata, yayin arrangama da jami’an tsaro a jiya Lahadi, yayin da a gefe guda tsaffin ‘yan majalisar dokokin kasar suka karfafawa mutane gwiwa kan cigaba da yiwa gwamnatin sojin da ta kawar da su bore.

Talla

Kusan watanni biyu kenan dubban ‘yan Myanmar suka shafe suna zanga-zangar adawa da juyin mulkin da sojojin kasar suka yi na kifar da gwamnatin tsohuwar shugabar su Aung San Su Kyii a ranar 1 ga watan Fabarairu.

A jiya lahadi ne kuma ‘yan majalisar dokokin kasar da a yanzu haka mafi akasarinsu ke boye, suka bukaci masu zanga- zanga da su zage damtse wajen ci gaba da yin bore, har sai sun cimma burin juyin juya halin komawa ga mulkin Dimokaradiyya.

Wasu 'yan kasar Myanmar mazauna India a birnin New Delhi, yayin zanga-zangar nuna goyon bayan masu yiwa sojoji bore.
Wasu 'yan kasar Myanmar mazauna India a birnin New Delhi, yayin zanga-zangar nuna goyon bayan masu yiwa sojoji bore. © Anushree Fadnavis / Reuters

Sai dai a wani sabon yunkuri na murkushe zanga-zangar, gwamnatin sojin ta Myanmar tayi shelar kafa dokar ta baci a manyan kuna biyu dake babban birnin kasar Yangon, da suka hada da Hlaing Tharyar da Shwepyitha.

Tun bayan barkewar tashin hankali a Myanmar daga farkon watan fanariru zuwa yanzu, masu zanga-zanga sama da 80 suka mutu yayin arrangama da jami’an tsaro.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.