Amurka - Asiya

Manyan jami'an Amurka sun fara ziyara a Asiya

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, daga dama da kuma Sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin daga hagu, yayin da Firaministan Japan Yoshihide Suga ke karbar bakuncinsu a ofishinsa dake birnin Tokyo.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, daga dama da kuma Sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin daga hagu, yayin da Firaministan Japan Yoshihide Suga ke karbar bakuncinsu a ofishinsa dake birnin Tokyo. AP - Kim Kyung-hoon

Shugaban ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon Lloyd Austin, da kuma sakataren harkokin wajen kasar Antony Blinken, sun fara ziyarar aikin ganawa da takwarorinsu na kasashen nahiyar Asiya, inda suka fara da kasar Japan.

Talla

Yanzu haka dai, manyan jami’an Amurkan biyu da suka yi balaguro a mabanbantan lokuta, sun hadu kasar Japan,  inda za su gana da Firaministan kasar Yoshihide Suga da mukarrabansa.

Bayan Japan, jami’an za kuma su yi tattaki zuwa Korea ta Kudu, inda daga nan sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin zai ziyarci India, yayin da shi kuma Sakataren Harkokin waje Anthony Blinken zai koma gida domin ganawa da wakilan kasar China.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, daga dama da kuma Sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin daga hagu bayan sauka a kasar Japan.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, daga dama da kuma Sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin daga hagu bayan sauka a kasar Japan. AP - Kim Kyung-hoon

Gwamnatin shugaba Joe Biden tace da gangan ta jinkirta tafiye-tafiyen jami’anta don cimma manufofin na Diflomasiya domin bada misalin takaita zirga-zirga a yayin da duniya ke kokarin dakile annobar Korona.

Tun kafin nasarar darewa Shugabancin Amurka Joe Biden ya sha alwashin gyara alakarsu da dukkanin kasashen da dangantakarsu tayi tsami a zamanin jagorancin tsohon shugaba Donald Trump.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.