Rohingya-Gudun Hijira

Dubban 'yan gudun hijiran Rohingya sun tsere daga sansaninsu saboda gobara

Sansanin 'yan gudun hijirar 'yan Rohingya da Gobara ta cinye.
Sansanin 'yan gudun hijirar 'yan Rohingya da Gobara ta cinye. - AFP/File

Wata mummunar gobarar da ta tashi a sansanin 'yan gudun hijirar Rohingya dake Bangladesh ta tilasta wa akalla mutane sama da 50,000 tserewa daga matsugunin, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 7.

Talla

Rahotanni sun ce akalla mutane kusan miliyan guda daga cikin 'yan kabilar Rohingya Musulmi ke zama a sansanin da ke yankin kudu maso gabashin Cox Bazar, kuma wannan ita ce gobara ta 3 da aka samu a wurin.

Masu aikin kashe gobara sun yi nasarar shawo kan  wutar da misalin karfe 12 na daren jiya, yayin da Shadat Hossain, jami’in kashe gobara ya tabbatar da mutuwar mutane 7 cikin su harda yara biyu da mace guda.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.