Lebanon-Siyasa

Jinkirin kafa gwamnati a Lebanon ya kawo zargin juna tsakanin jagorin kasar

Saad Hariri, firaministan Lebanon.
Saad Hariri, firaministan Lebanon. AP Photo/Hussein Malla

Firaministan Lebanon Saad Hariri da shugaban kasa Michel Aoun na zargin junan su dangane da tsaikon da aka samu wajen kafa sabuwar gwamnati, bayan kwashe makwanni ana tintibar juna ba tare da kulla yarjejeniya ba.

Talla

Gazawar shugabannin biyu wajen amincewa juna domin kafa sabuwar gwamnati a taron da suka gudanar jiya Litinin ta dakushe duk wata fata da ake da ita na kawo karshen tsaikon da ake samu.

Hariri yace ya bukaci shugaban kasar da ya saurari koke koken jama’a domin bada damar zabo kwararrun mutane domin kafa gwamnati yaki.

Sai dai nan take fadar shugaban kasar taki amincewa da zargin.

Shugaban mabiya Shia na kasar Hassan Nasrallah yace kafa gwamnati mai dauke da kwararru ba tare da Yan siyasa ba ba zai taimakawa kasar ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.