Myanmar-Arangama

Jami'an tsaron Myanmar sun kashe masu zanga-zanga sama da 20

Masu zanga-zanga a myanmar na arcewa yayin wata dirar mikiya da sojoji suka yi musu.
Masu zanga-zanga a myanmar na arcewa yayin wata dirar mikiya da sojoji suka yi musu. REUTERS - STRINGER

Jami’an tsaro sun kashe masu zanga-zanga 24 a yau Asabar, a daya daga cikin ranaku mafi muni tun da sojoji suka hambarar da gwamnatin kasar,  bayan da hukumomin suka yi amfani da karfi fiye da kima a ranar bikin tunawa da dakarun kasar.

Talla

Kasar ta fada cikin hali na tashin hankali tun da janar-janar din soji suka hambarar da gwamnatin Aung San Suu Kyi a watan Fabrairu, lamarin da ya jaanyo zanga zangar masu neman a maido da dimokaradiya.

An gudanar da wani gagarumin faretin soji da safiyar yau Asabar a babban birnin kasar, Naypyidaw, inda jagoran masu juyin mulkin, Min Aung Hlaing ya gabatar da jawabi yana mai kashedin cewa ba zai lamunci abin da ya kira ayyukan ta’addanci ba.

Ya zuwan tsakar ranar Asabar, masu zanga- zangar sun ci gaba da fitowa a sassan Myanmar, inda kamfanin dillancin labaran Faransa ya tantance mamata 24, amma kafofin yada labaran kasar sun bayyana adadi kasa da haka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.