China

Shirin aikewa da tawaga zuwa yankin Xinjiang

Mata 'yan kabilar Uighur na fuskantar cin zarafin hana su haihuwa a Xianjing na China
Mata 'yan kabilar Uighur na fuskantar cin zarafin hana su haihuwa a Xianjing na China REUTERS/Petar Kujundzic

Majalisar DimkinDuniya ta ce yanzu haka tana kan tattaunawa da mahukuntan kasar Cnina don samun izinin aikewa da tawaga zuwa yankin Xinjiang inda ake tsare da ‘yan kabilar Uighar saboda dalilai masu nasaba da addini.

Talla

Antonio Guterres

Antonio Guterres, Sakatary MDD
Antonio Guterres, Sakatary MDD MICHAEL TEWELDE AFP/File

an jima ana tattaunawa tsakanin wakilan hukumar kula da kare hakkin bil’adama ta Majalisar da kuma jami’an gwamnatin China, domin kai ziyara a yankin, a dai-dai lokacin China ke fuskantar suka daga kasashen yammacin Duniya dangane da wannan batu.

Wata cibiyar bincike kan lamurran yau da kullum mai zaman kanta dake kasar Australia ASPI, tace gwamnatin China ta rusa dubban Masallatai a yankin Xinjiang.

Rahoton da cibiyar ta ASPI ta wallafa  shi ne na baya bayan nan daga cikin jerin rahotanni da kungiyoyin kare hakkin da adam kan yadda hukumomin kasar ta China ke cin zarafin Musulmi da ma sauran kabilu marasa rinjaye a yankin na Xinjiang.

Sabon rahoton ya kara da cewar babu wani wurin ibada na mabiya addinin Buddah ko kuma Mujami’u da hukumomin na China suka taba, yayinda suka rushe akalla kashi 1 bisa 3 na wuraren ibada na Musulmi, musamman biranen Urumqi da Kashgar da ke yankin na Xinjiang.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.