Saudiya-Isra'ila

Dangantaka da Israila zai haifar da cigaba a Gabas ta Tsakiya – Saudiya

Yarima mai jiran gado na Saudiya Mohammed bin Salman.
Yarima mai jiran gado na Saudiya Mohammed bin Salman. REUTERS - Handout .

Gwamnatin Saudi Arabiya ta ce kulla dangantaka da Israila zai haifar da gagarumin cigaba a Gabas ta Tsakiya amma hakan zai faru ne kadai idan aka sasanta rikicin Israilan da Falasdinawa ta hanyar kafa kasar Falasdinu.

Talla

A karkashin sabuwar yarjejeniyar da gwamnatin tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da aka yi wa lakabi da ‘Abraham Accord‘ wasu kasashen Larabawa guda 4 da suka hada da Daular larabawa da Bahrain da Sudan da kuma Morocco sun amince su kulla hulda da Israilar.

Sai dai Ministan harkokin wajen Saudi Arabia Yarima Faisal bin Farhan ya ce duk wata hulda da kasar za ta kulla da Israila zai zo ne sakamakon yarjejeniyar zaman lafiyar da zata kulla da Falasdinawa.

Ministan ya ce yana da kyakyawar fatar kulla huldar da Isra'ila zai samar da cigaba a yankin baki daya, kuma zai taimakawa tattalin arziki da kuma jin dadin jama’ar yankin.

Kasar Saudi Arabia na ci gaba da jaddada matsayin ta na cewar ba za ta amince da kasar Israila ba har sai ta sasanta da Falasdinawa.

A watan Nuwambar bara an ruwaito cewar Firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya gana da Yarima Mohammed bin Salman amma daga bisani gwamnatin Saudiya ta musanta rahotan.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.