Myanmar

Jami'an tsaron Myanmar sun bude wuta kan masu zanga-zanga tare da kashe 4

Wani daga cikin Masu zanga zangar adawa da juyin mulki a Myanmar  da sojoji suka raunata  ke samun kulawar liktoci a 27/03/2021.
Wani daga cikin Masu zanga zangar adawa da juyin mulki a Myanmar da sojoji suka raunata ke samun kulawar liktoci a 27/03/2021. AP

Jami'an tsaron Myanmar sun bude wuta kan masu zanga-zangar neman demokradiyya, inda suka kashe mutane hudu, a cewar wani mai zanga-zangar da kuma kafofin yada labarai, yayin da sojoji suka karfafa yunkurinsu na kawo karshen adawar tare da fitar da sammacin kame ga masu sukar su ta intanet.

Talla

Duk da kisan da jami’an tsaro suka yi wa mutane sama da 550 tun bayan juyin mulkin ranar 1 ga Fabrairu, masu zanga-zangar na fitowa kowace rana, galibi a kananan kungiyoyi a kananan garuruwa, don nuna adawa da mulkin soja.

Jaridar News Now ta kasar Myanmar tace, Jami'an tsaro a garin Monywa da ke tsakiyar kasar sun yi harbi kan taron jama'a inda suka kashe mutane ku.

Yayin da wani mai zanga-zangar a Monywa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyanawa wa kamfanin dillacin labaran Reuters ta hanyar sakon intanet yana cewa "Sun fara harbe-harbe ba tare da kakkautawa  ba "Mutane sun ja da baya da sauri sun sanya ... shinge, amma harsashi ya samu wani mutum a gabana a kai. Ya mutu nan take."

Shaidar gani da ido

An harbe wani mutum har lahira a garin Thaton da ke kudancin kasar, in ji kafar yada labarai ta yanar gizo ta Bago Weekly Journal. Kafafen yada labaran sun bayar da rahoton cewa an kashe mutum daya a garin Bago amma daga baya ta ce mutumin ya ji rauni bai mutu ba.

‘Yan sanda da mai magana da yawun mulkin sojan ba su amsa kiran waya ba don jin ta bakinsu.

Kungiyar nan mai rajin taimakawa kungiyar fursunonin siyasa, a wata sanarwa da ta fitar a safiyar yau, ta ce jami’an tsaron sun kashe mutane 550, 46 daga cikinsu yara kanana, tun lokacin da sojoji suka hambarar da zababbiyar gwamnati karkashin jagorancin Aung San Suu Kyi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.